Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya ɗansa, Seyi Tinubu, murnar cika shekaru 40 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai natsuwa, jajircewa da kwarewa wanda ya keɓanta wajen kawo ci gaba ga ƙasa da al’umma.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙasar ya sanya hannu kansa a ranar Lahadi, ya ce: “Yau da kake cika shekaru 40, ina gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa rayuwarka da irin mutumin da ka zama.
Shugaba Tinubu ya kara da cewa ɗansa tun yana ƙarami yake nuna halin jagoranci da hangen nesa, yana mai yabawa da yadda yake “mai sauya ra’ayoyi zuwa ayyuka da ƙalubale zuwa damar cigaba.”