Manoman rake a Kano sun yi asarar sama da Naira biliyan 2

0
19

Manoman rake a Kano sun yi asarar sama da Naira biliyan 2

Manoman rake a jihar Kano sun bayyana cewa wata sabuwar cuta ta addabi gonakinsu, ta kuma haddasa musu babbar asara da ta kai kusan Naira biliyan biyu, lamarin da ke barazana ga daruruwan manoma a yankunan karkara.

A cewar wasu manoma a ƙauyen Gamadan, wanda ke cikin ƙaramar hukumar Kura, cutar ta shafi yawancin gonakin rake a bana, inda suka ce yawancin amfanin gona ya lalace gaba ɗaya.

“Mun yi noman rake da duk ƙarfinmu da dukiyarmu a bana, amma cutar ta hallaka yawancin gonaki. Mutane da yawa sun rasa abin da suka shuka,” in ji wani manomi, Idris Musa Kura.

Rahotanni sun nuna cewa cutar ta bazu zuwa wasu ƙauyuka da ke kusa da Gamadan, ciki har da Tofa, Dukawa, Kunshama, Danhassan, da Garin Kaya, duk a yankin Kura.

Wani ɗan kasuwa a yankin, Alhaji Kabiru Sulaiman, ya ce idan gwamnati ba ta tallafawa manoman ba, kasuwa za ta fuskanci ƙarancin rake da hauhawar farashi. Idan ba a ɗauki mataki ba, nan gaba ba za a samu rake a kasuwa ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here