Gwamnatin Kano ta fitar da gargadi kan yaduwar zazzabin Lassa

0
17

Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da gargadi ga jama’a kan yiwuwar yaduwar zazzabin Lassa, yayin da ƙasar nan ke shiga lokacin da ake samun yawaitar kamuwa da ita.

Daraktan cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta jihar (KNCDC), Dr. Muhammad Adamu Abbas, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, inda ya ce gargadin ya biyo bayan shawarar da Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaɗuwa ta Kasa (NCDC) ta bayar game da yiwuwar ƙaruwar a kamuwa da cutar daga watan Oktoba zuwa Mayu.

Ya ce saboda yanayin muhalli da tsarin rayuwa na Kano, jihar na cikin waɗanda ke da haɗarin kamuwa da cutar. Ya kuma bukaci jama’a su kiyaye tsafta, su rufe abinci da kyau, tare da toshe kofofin da beraye ke iya shiga gidajen mutane.

An shawarci jama’a da su garzaya asibiti idan suna fama da zazzabi mai tsanani ko alamomin cutar.

Dr. Abbas ya ce ana gudanar da wayar da kai da kuma yaƙi da beraye a wasu yankuna da aka fi ganin haɗari, a karkashin tsarin “One Health” na jihar.

Ya ƙara da cewa cutar Lassa fever ana iya kauce mata da kuma warkewa daga gare ta idan aka gano da wuri, don haka ya nemi hadin kai daga al’umma wajen bin shawarwarin lafiya.

Cutar Lassa fever cuta ce mai sa zazzabi wadda ke yaduwa ta hanyar abinci ko ma’amala da berayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar. Ana iya kamuwa da ita daga mutum zuwa mutum ta hanyar jini ko ruwa daga jikin wanda ya kamu da cutar.

Alamomin cutar sun haɗa da zazzabi mai tsanani, ciwon wuya, ciwon kirji ko ciki, amai, gudawa da kuma zubar jini. Likitoci sun ce gano cutar da wuri yana ƙara yuwuwar samun lafiya cikin sauƙi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here