ASUU ta tsunduma yajin aiki a faɗin Najeriya 

0
69

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta sanar da shiga yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu a dukkan jami’o’in gwamnati daga daren Litinin, 13 ga Oktoba, 2025.

Shugaban kungiyar na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja ranar Lahadi.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika wasu muhimman buƙatun ƙungiyar duk da dogon tattaunawa da aka yi.

ASUU na neman gwamnatin ta aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2009, ta samar da isasshen kuɗi domin farfaɗo da jami’o’i, ta biya alawus ɗin malamai, tare da inganta walwalarsu.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a kwanakin baya cewa gwamnati ta saki Naira biliyan 50 domin biyan alawus ɗin malamai da kuma ware ƙarin Naira biliyan 150 a kasafin kuɗin 2025 don gyaran jami’o’i.

Sai dai ASUU ta ce, har yanzu gwamnatin ba ta nuna cikakken niyyar magance matsalolin ba, abin da ya sa ta ɗauki matakin wannan yajin aikin gargadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here