’Yan Sanda Sun Ceto Mutane 10 da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Su a Kaduna

0
15

Rundunar ’yan sanda reshen Kaduna ta tabbatar da cewa ta ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su tun watanni hudu da suka gabata a ƙaramar hukumar Kagarko.

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka ceto akwai yara masu shekaru ɗaya, uku, da kuma 13. An sace su ne lokacin da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kushe Makaranta suka kuma kai su dajin da ke kusa da Rijana.

DSP Hassan ya ce aikin ceton ya samu ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sanda, DSS, da sojojin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here