Jihar Kano ta samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya

0
24

Rahotanni sun nuna cewa Jihar Kano tana samun ƙaruwa a kuɗaɗen da ake rarrabawa daga asusun tarayya a wannan shekarar ta 2025. 

Wannan yana nuna cewa ana samun cigaba a tattalin arzikin ƙasa, musamman daga kudaden da ake samu daga fannin mai da kuma waɗanda ba na mai ba.

Binciken da aka yi daga bayanan hukumomin gwamnati ya tabbatar da cewa a cikin watanni takwas na farko na shekarar 2025, gwamnatin jihar Kano da ƙananan hukumomi 44 na jihar suna samun ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya.

Masana sun ce wannan al’amari yana nuna cewa Kano tana cikin wani lokaci na kwanciyar hankali a fannin kuɗi, wanda hakan na iya taimakawa wajen inganta ayyukan raya ƙasa da walwalar jama’a.

Kamar yadda alkaluma suka nuna ƙananun hukumomin Kano sun karɓi kuɗin da yakai Naira biliyan 348.2, daga gwamnatin tarayya a cikin watanni 8.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here