Jarirai Mata Na Iya Yin Jinin Al’ada — Likita

0
14

Wata likitar yara mai suna Dr. Ayobola Adebowale, wacce aka fi sani da Your Baby Doctor, ta bayyana cewa wasu jarirai mata na iya yin ɗan zubar jini bayan haihuwa abin da ake kira “pseudo menstruation” ko “neonatal menstruation” a fannin likitanci.

A cewar rahoton jaridar PUNCH, likitar ta ce wannan yanayi yana faruwa ne saboda canjin kwayoyin halitta (hormones) da jaririyar ke fuskanta bayan an haife ta, kuma ba cuta ba ce.

Dr. Adebowale ta bayyana cewa yayin da jaririya ke cikin mahaifiyarta, tana samun tasirin kwayoyin halittar uwa sosai. Amma bayan haihuwa, lokacin da tasirin ya ragu kwatsam, sai hakan ya jawo abin da ake kira withdrawal bleeding wato fitar wani jini mai kama da al’ada.

Ta shawarci iyaye da kada su firgita idan suka ga irin wannan jini a wajen jariransu, domin abu ne na dabi’a kuma baya buƙatar magani.

Ta ce, “Ku kwantar da hankalinku. Wannan jinin ba matsala ba ce, kuma yawanci yana daina fita da kansa cikin ‘yan kwanaki”.

Masana a fannin likitanci sun tabbatar da cewa wannan yanayi yawanci yana faruwa ne a mako na farko bayan haihuwa, kuma babu abin da zai tayar da hankali muddin babu wasu alamomin rashin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here