Harajin Shugaban Amurka Ya Karya Kasuwar Kirifto

0
21

An samu girgizar kasuwa bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yiwuwar sanya haraji kan kayayyakin China, abin da ya haifar da karyewar farashin hannayen jari da kuɗaɗen intanet na kirifto.

Farashin Bitcoin ya fadi da sama da kashi 10 cikin 100 kafin daga baya ya ɗan farfaɗo. 

Haka kuma sauran kuɗaɗen kirifto kamar Ethereum da Solana suma sun shiga halin koma-baya.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin China ta sanar da tsauraran dokoki kan fitar da ma’adanan da ake amfani da su wajen ƙere-ƙeren fasahar zamani zuwa Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here