Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba wato SSANU da NASU sun gudanar da zanga-zangar lumana a wasu jihohin ƙasar nan, ciki har da Kano, Kaduna da Nasarawa, don nuna rashin jin daɗinsu kan riƙe albashinsu da rashin aiwatar da yarjejeniyar 2009.
A Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Sabo Balarabe Wudil, Mataimakin Shugaban SSANU na ƙasa (Arewa maso Yamma), ya ce gwamnati ta kasa biyan buƙatun da aka dade ana nema ciki har da:
Albashin watanni biyu da aka riƙe tun lokacin yajin aikin 2022
Rashin biyan Naira biliyan 40 daga cikin Nairs biliyan 50 da aka amince a matsayin kudaden alawus na ma’aikatan.
Da kuma rashin aiwatar da yarjejeniyar 2009.
Ya ƙara da cewa:
“Mun gaji da alƙawura. Wannan zanga-zanga ba ƙarshe ba ce, idan gwamnati ta yi shiru, za mu ɗauki mataki mafi tsanani.”
A ABU Zaria da Federal University Lafia (FULAFIA), ma’aikata sun fito zanga-zangar.
Shugaban SSANU na FULAFIA, Comrade Daniel Dajen, ya ce gwamnati ta saba yarjejeniya da ke buƙatar a sake tattaunawa kan albashi duk bayan shekara biyar.


