Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar zaɓe INEC

0
43

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunan Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga Jihar Kogi a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), bayan karewar wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya kammala aikinsa a watan Oktoba 2025.

An tabbatar da nadin ne a taron Majalisar Ƙasa da aka gudanar a ranar Alhamis, inda dukkan mambobin majalisar suka amince da shi bayan gabatarwar shugaban ƙasa.

A wata sanarwa da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya bayyana cewa an zaɓi Farfesa Amupitan ne bisa cancanta da gaskiya, ba tare da la’akari da siyasa ba.

Tinubu ya bayyana sabon shugaban INEC ɗin a matsayin ƙwararren masanin doka da mai kishin gaskiya, wanda ya tabbatar da jajircewarsa wajen kare mutuncin cibiyoyin gwamnati.’

A cewar sanarwar, shugaban ƙasa zai tura sunan Farfesa Amupitan zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

An haifi Farfesa Amupitan a ranar 25 ga Afrilu, 1967, a garin Ayetoro Gbede, Ƙaramar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi. Yana aiki a matsayin Farfesa a Sashen Shari’a na Jami’ar Jos (UNIJOS) kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar a Harkokin Gudanarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here