Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da sunayen waɗanda zai iya nada wa matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a zaman Majalisar Koli ta Ƙasa da ake gudanarwa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Zaman majalisar, wanda aka fara da misalin ƙarfe 1:29 na rana a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, ya samu halartar manyan jagororin ƙasa da tsofaffin shugabanni.
Rahotanni daga jaridar The Punch sun bayyana cewa shugaban ƙasa ya gabatar da mutane uku domin tantancewa a matsayin magajin Farfesa Mahmood Yakubu wanda wa’adinsa ya ƙare.
Mutanen sune:
Farfesa Joash Amupitan,
Mai shari’a Abdullahi Mohammed Liman,
Da Farfesa Lai Olurede.
Dukkan masu neman wannan mukami ƙwararru ne a fannin shari’a da ilimi, kuma ana sa ran majalisar za ta tantance su kafin a yanke hukunci na ƙarshe kan wanda zai zama sabon shugaban INEC.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda za a inganta tsarin zaɓe a Najeriya kafin babban zaɓen da ke tafe.


