Rikicin Boko Haram ya janyo asarar Naira triliyan 14.5 a Najeriya–UNICEF

0
24

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya ta yi asarar fiye da dala biliyan 10 kimanin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon tasirin rikicin Boko Haram da ya daɗe yana addabar Arewa maso Gabas.

Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana haka yayin ƙaddamar da sabon shirin tallafawa yara da rikici ya shafa a Maiduguri.

Ta ce binciken da UNICEF ya gudanar ya nuna cewa rikicin ya rage ƙarfin tattalin arziki, ya kuma durƙusar da samun kuɗin shiga da damar aiki ga iyalai da matasa, musamman ’yan mata.

A cewar ta, fiye da yara 1,000 sun fara amfana da horo a sana’o’i kamar dinki, gyaran mota, ƙera takalma da sauran fannoni a wuraren horo da ke Maiduguri, Bama, Biu, Damboa da Konduga.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Borno, Abba Wakilbe, ya gode wa UNICEF bisa goyon bayan da yake bai wa gwamnati wajen farfaɗo da rayuwar yaran da rikici ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here