Najeriya tana bin ƙasashen Benin da Togo bashin dala miliyan 8.5 na wutar lantarki

0
81

Najeriya tana bin ƙasashen Benin da Togo bashin dala miliyan 8.5 na wutar lantarki

Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta bayyana cewa Najeriya tana bin ƙasashen Benin da Togo, bashin kuɗin wutar lantarki da suka karɓa, wanda ya kai dala miliyan 8.5 a zangon watanni na biyu na shekarar 2025.

A cewar rahoton NERC, kasashe shida da ke karɓar wutar lantarki daga Najeriya sun biya dala miliyan 9.01 kacal daga cikin jimillar dala miliyan 17.54 da aka caje su. Wannan yana nufin cewa an biya kaso 51.33 cikin 100 na kuɗin da ake binsu, inda wasu ƙasashen ba su biya komai ba.

Rahoton ya nuna cewa kamfanin wutar Benin, Société Béninoise d’Énergie Électrique (SBEE), ya biya wani ɓangare na bashin da ake binsa, yayin da kamfanin Togo, Compagnie Energie Electrique du Togo (CEET), bai biya ko kwabo daga cikin dala miliyan 4.31 da ake binsa ba. Sai dai kamfanin wutar Nijar, NIGELEC, ya biya dala miliyan 2.59 daga cikin dala miliyan 3.71 da ake binsa.

NERC ta ce wannan rashin biyan kuɗi daga ƙasashen waje da wasu kamfanonin cikin gida yana kawo cikas ga ci gaban kasuwar wutar lantarki ta Najeriya, tare da shafar ikon kamfanonin samar da wuta da masu kula da rarrabawa wajen tabbatar da ingantaccen wutar lantarki a gida da ƙetare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here