Gyaran tattalin arziƙin Tinubu bai amfanar da talakawa ba–Bankin Duniya

0
38
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Gyaran tattalin arziƙin Tinubu bai amfanar da talakawa ba–Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa duk da irin gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Najeriya ke aiwatarwa, mafi yawan ’yan ƙasa har yanzu ba su ji sauyi a rayuwarsu ba, inda kimanin mutane miliyan 139 ke ci gaba da rayuwa cikin talauci.

Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rahoton irin cigaban da ake samu a ƙasar a birnin Abuja.

Ya ce Najeriya ta samu ci gaba wajen daidaita musayar kuɗi, rage bashi da kuma sauƙaƙe hauhawar farashi, amma wadannan nasarorin basu kai ga inganta rayuwar jama’a ba.

Verghis ya kara da cewa hauhawar farashin abinci, raguwar ƙarfin siye da rashin daidaito wajen rabon albarkatu, na daga cikin manyan abubuwan da ke jefa mutane cikin ƙuncin tattalin arziki.

A cewarsa, talauci ya ƙaru tun daga shekarar 2019 sakamakon wasu manufofi marasa kyau da kuma tasirin annobar COVID-19, lamarin da ya ci gaba duk da sabon tsarin kudi da gwamnati ta aiwatar.

Shi ma Samer Matta, babban masani kan tattalin arziki na Bankin Duniya a Najeriya, ya bayyana cewa duk da ƙarin kudaden shiga da ake samu cikin 2025, akwai matsala wajen yawan cire kuɗaɗe daga hukumomin tattara haraji, wanda ke rage tasirin gyare-gyaren tattalin arzikin ga al’umma.

Ya bukaci gwamnati ta tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake samu suna zuwa ga ayyukan da zasu inganta rayuwar ’yan ƙasa kai tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here