Gwamnatin Kano zata ɗaura wa mutane 2,000 auren gata

0
23

Gwamnatin Jihar Kano ta shirya gudanar da bikin ɗaura auren gata ga akalla ma’aurata dub biyu (2,000) domin ƙarfafa ɗa’a da walwalar al’umma a fadin jihar.

An bayar da umarnin shirya wannan gagarumin bikin ne ta hannun Rundunar Hisba ta Jihar Kano, wacce ta fara shiri don ganin an gudanar da lamarin cikin nasara.

Mataimakin Kwamandan Rundunar Hisba, Sheikh Mujahid Aminudeen, ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da jaridar PUNCH a yau Alhamis, inda ya bayyana cewa shirin na nufin rage aikata laifuka, tallafawa marasa galihu musamman zawarawa, mata da kuma waɗanda ke son aure amma ba su da hali.

Ya ce, duk ma’auratan da ke son shiga cikin shirin za su yi rajista da hukumar Hisba tare da yin gwaje-gwajen lafiya kamar na cuta mai karya garkuwar jiki, ciwon hanta, da gwajin jini domin tabbatar da lafiyarsu kafin a ɗaura musu aure.

Gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 2.5 a cikin kasafin kuɗin shekara ta 2025 domin aiwatar da wannan shiri, a matsayin wani ɓangare na manufarta ta tallafa wa al’umma da kuma tabbatar da ingantacciyar rayuwa mai ɗa’a a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here