Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗe fiye da naira biliyan huɗu da ake zargin tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta aikata.
Shugaban hukumar, Saidu Yahaya, ya ce binciken ya biyo bayan ƙorafi da aka shigar musu, inda ake zargin cewa an ɗauki kuɗaɗen gwamnatin Kano ta zamanin Ganduje, aka saka su a tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port.
A cewar Yahaya, mun fara bincike kan wasu kuɗaɗe da aka cire daga asusun gwamnatin Kano aka saka su a cikin Dala Inland Dry Port. Jimillar kuɗin ya kai sama da naira biliyan huɗu, kuma an ɗauke su ne a lokacin mulkin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.”
Da aka nemi karin bayani daga tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar kuma tsohon shugaban ma’aikatan Ganduje, Muhammad Garba, ya bayyana cewa, wannan maganar tana gaban kotu, don haka bai san irin binciken da ake nufi ba.
Yace da ya tuntuɓi tsohon Ganduje, ya ce babu abin da ke damunsa, domin irin waɗannan binciken ba sabon abu ba ne.”
Hukumar PCACC ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da gaskiyar batun, tare da tabbatar da cewa an yi adalci ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.


