Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya shiga sahun masu kira ga gwamnatin tarayya da ta saki Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biapra (IPOB), inda ya bayyana tsare shi na dogon lokaci a matsayin take hakkin ɗan Adam.
A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukan sada zumuntarsa a ranar Alhamis, ya ce:
“Tsare Nnamdi Kanu duk da umarnin kotu na bayar da belinsa cin zarafi ne ga doka da adalci. Wannan lamari yana ci gaba da zama tabo ga ƙasar da ke ikirarin bin tsarin doka.”
Atiku ya kara da cewa yana gozon bayan kiran da dan gwagwarmaya Omoyele Sowore ke jagoranta, wanda ke neman a saki Kanu nan take ko kuma a gurfanar da shi a kotu cikin gaskiya da adalci.
An kama Nnamdi Kanu a ƙasar Kenya a shekarar 2021, daga nan aka kawo shi Najeriya inda yake hannun Hukumar DSS, yana fuskantar tuhumar ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.