Ƙudirin samar da jihar Ibadan ya tsallake karatu na biyu a majalisa

0
24

Majalisar Wakilai  ta amince da kudirin da ke neman kafa sabuwar jihar Ibadan daga cikin Jihar Oyo, bayan karanta shi karo na biyu a zaman majalisar na yau Alhamis.

Kudirin wanda dan majalisa Abass Adigun, mai wakiltar mazabar Ibadan North-East/Ibadan South-East, ya dauki nauyi, yana neman a gyara kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 domin baiwa Ibadan damar zama jiha mai cikakken iko.

Yayin gabatar da kudirin, Adigun ya ce matakin yana da muhimmanci wajen tabbatar da daidaito a cikin tsarin tarayya da kuma samar da damar ci gaba ga al’ummar Ibadan, wadanda suka daɗe suna fatan samun jiharsu ta kansu.

Ya kara da cewa Ibadan na da yawan jama’a da fadin kasa da ya wuce na wasu jihohi a ƙasar nan. “Karamar hukuma guda a Ibadan ta fi wasu karamar hukumomi uku a Jihar Bayelsa girma,” in ji shi.

Sai dai wannan kalma tasa ta jawo cece-kuce daga dan majalisa Obuku Ofurji, mai wakiltar mazabar Yenagoa/Opokuma ta Jihar Bayelsa, wanda ya bayyana maganar a matsayin abin raini da rashin girmama jiharsa. Adigun ya nemi afuwa, amma ya dage cewa bayanin nasa gaskiya ne.

An mika kudirin ga Kwamitin Gyaran Tsarin Mulki na Majalisar Wakilai domin ci gaba da nazari da tantancewa.

A baya-bayan nan, Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, ya roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka wajen kafa Jihar Ibadan kafin shekarar 2027, yayin bikin nadinsa a matsayin Olubadan na 44.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here