Majalisar Dattawa ta amince da dokar da za ta hana ɗan Najeriya da aka tabbatar da laifi a ƙasashen waje mallakar fasfo na tsawon shekaru goma.
An amince da wannan kudiri ne a zaman majalisar na ranar Talata, a matsayin mataki na dakile ayyukan da ke bata sunan Najeriya a kasashen ƙetare.
Wannan dokar na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na inganta ɗabi’un ‘yan ƙasa da kuma kare mutuncin Najeriya a idon duniya.