Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da mayar da jabun takardun kammala karatu da karya hanyar mulki a Najeriya.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya ce murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, saboda zargin jabun takardu, ya nuna “rashin ɗabi’a mai kyau” a cikin gwamnatin Tinubu.
Ya kuma soki jami’an tsaro na farin e DSS da gazawa wajen tantance jami’an gwamnati, yana cewa “hukumar da ta hana El-Rufai mukami ce ta amince da Uche Nnaji.”
Atiku ya ƙara da cewa rikicin takardun shugaban ƙasa Tinubu ya gurbata tsarin mulki, inda ya ce:
> “Idan wanda ke mulki yana da matsalar gaskiya, to karya ce zata zama al’ada a gwamnatin sa.”
Ya bukaci a gudanar da bincike kan takardun dukkan ministoci da shugaban ƙasa, yana mai cewa:
> “Sai an dawo da gaskiya cikin gwamnati sannan Najeriya za ta fita daga halin lalacewa.”