Tsohon shugaban Kwalejin CAS Kano, Dr. Nasiru Ibrahim Dantiye, ya rasu yana da shekaru 76.
Majiyoyi daga iyalansa sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu a ranar Talata a garin Kano bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ɗan uwan sa wanda tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, ne Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa za a gudanar da sallar jana’izarsa a fadar Sarkin Kano, Kofar Kudu.
Dr. Dantiye ya shugabanci Kwalejin CAS tsakanin 1995 zuwa 1996, sannan ya yi aiki a matsayin Daraktan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano (Kano State Polytechnic) kafin daga bisani ya koma Jami’ar Northwest, inda ya koyar da tarihin Najeriya.
Haka kuma, yana daga cikin ma’aikatan farko na hukumar National Examinations Council (NECO), inda ya taka rawa a matsayin Darakta tun farkon kafa hukumar.
Marigayin ya bar mata ɗaya, ’ya’ya uku da jikoki.
Allah ya jikansa da rahama, ya kuma bawa iyalansa hakurin jure wannan rashi.