Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai ƙaru da kashi 4.4 cikin ɗari a shekarar 2027, wanda ya fi hasashen shekarar 2025 da aka ce zai kasance kashi 4.2 cikin ɗari.
Bankin ya ce wannan ci gaba zai samu ne ta hanyar sashen ayyuka, tare da taimakon noman gona da masana’antu da ba na man fetur ba.
Wannan bayani ya fito ne daga rahoton da aka fitar a birnin Abuja mai taken “Daga manufofi zuwa talakawa: yadda gyare-gyare za su amfanar da jama’a”.
A cewar wani babban jami’in bankin, Samer Matta, hauhawar farashin kaya na raguwa a hankali, amma har yanzu hauhawar tana da yawa. Ya ce akwai bukatar gwamnati ta ci gaba da tsaurara matakan kudi da aiwatar da gyare-gyare domin rage tsadar abinci, wanda shi ne babban kalubale ga talakawa.
Sai dai bankin ya bayyana cewa duk da wannan cigaba, yawancin ‘yan ƙasa har yanzu suna fama da talauci da tsadar abinci, inda farashin abinci ya ninka fiye da sau biyar tsakanin shekarar 2019 zuwa 2024.
A nasa bangaren, Mathew Verghis, wakilin Bankin Duniya a Najeriya, ya ce gwamnati ta ɗauki matakai masu ƙarfi wajen daidaita tattalin arziki, amma ya jaddada cewa nasara ta gaskiya ita ce yadda waɗannan gyare-gyare za su inganta rayuwar talakawa.