Matar Aure Ta Rataye Kanta a Jigawa

0
26

Matar Aure Ta Rataye Kanta a Jigawa

Wani lamari mai tayar da hankali ya auku a kauyen Sumore da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa, inda wata matar aure mai suna Adama Hannafi, mai shekaru 30, ta rataye kanta har lahira.

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta daÉ—e tana fama da matsalar kwakwalwa, kafin a same ta a rataye da rana tsaka a bishiya cikin garin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai gawar zuwa asibitin gwamnati na Dutse inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya roƙi al’umma su riƙa nuna kulawa ga masu fama da damuwa, tare da neman taimakon likitoci ko ƙwararru kafin lamarin ya kai ga janyo asarar rayuka.

Marigayiyar ta bar mijin ta da ’ya’ya huɗu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here