Masanin shari’a ya bayyana mafita a kan saɓanin gwamnatin Kano da kwamishinan ƴan sanda

0
28

Idan za’a iya tunawa a jihar Kano, an samu rashin jituwa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, bayan kwamishinan ya gaza halartar bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2025, lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin bangarorin siyasar Kano.

A yayin tattaunawar da muka yi da lauya Barista Abdulkadir Alhaji Sani, Mataimaki na ɗaya na Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law Society – NLS), ya bayyana cewa doka ta bai wa gwamna damar bayar da umarni ga kwamishinan ‘yan sanda akan duk wani abu da ya shafi tsaron al’umma. Sai dai ya ce kwamishinan ‘yan sanda na da ‘yancin kin bin umarni idan abin da gwamnan ya nema ya saba da ka’idar aiki, tare da sanar da babban Sufeton ‘Yan Sanda na ƙasa.

Barista Abdulkadir ya kuma ce siyasa na daga cikin manyan dalilan da ke janyo irin wannan rashin jituwa. Ya ce banbancin jam’iyyar siyasa tsakanin gwamnatin Kano da gwamnatin tarayya na iya taka rawa wajen haifar da wannan matsala.

“Idan aka bar wannan rikici haka, zai iya kawo matsala ga harkar tsaro a Kano,” in ji Barista Abdulkadir. “A halin yanzu, akwai bukatar haɗin kai tsakanin gwamnatin jiha da jami’an tsaro domin kare zaman lafiya, musamman a yanayin da ake ciki na masu ƙwacen waya da ƴan daba.”

Lauyan ya kara da cewa, idan Gwamna Abba Kabir Yusuf na ganin kwamishinan ‘yan sanda ya aikata wani abu da ya kawo sabani tsakaninsu, yana da damar neman a sauya shi ta hanyar miƙa buƙatar sa zuwa ofishin babban Sufeton ‘Yan Sanda.

Sai dai ya jaddada cewa bai dace da kwamishinan ‘yan sanda ya janye jami’ansa daga filin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai ba, domin hakan na iya nuna rashin haɗin kai tsakanin gwamnati da jami’an tsaro, ko kuma hakan ka’iya zama cin zarafi ga gwamnan Kano.

A cewar Barista Abdulkadir Alhaji Sani, Mataimaki na ɗaya na Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law Society – NLS), hanya mafi dacewa wajen samar da daidaito akan wannan matsala ita ce a samar da sasanci tsakanin bangarorin biyu ko kuma a kawo sabon kwamishina a jihar Kano tare da ɗauke kwamishina Bakori, domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here