Majalisar wakilai ta yi watsi da wani kudiri daga majalisar dokokin Amurka da ke zargin cewa gwamnati na da hannu wajen kashe Kiristoci a Najeriya.
‘Yan majalisar sun bayyana cewa babu wata barazana ta gwamnati ga Kiristoci ko wani addini, tare da jaddada cewa matsalolin tsaro a Najeriya sun Musulmi da Kirista, kuma suna da nasaba da ta’addanci, fashi da makami, rikicin manoma da makiyaya da rikice-rikicen kabilanci, ba wai addini kawai ba.
Kudirin, wanda Sanata Ted Cruz na Amurka ya gabatar mai suna Nigeria Religious Freedom Accountability Act of 2025, yana neman hukunta jami’an Najeriya da ake zargi da tauye ‘yancin addini, tare da kiran a sanya takunkumi ga waɗanda ke aiwatar da dokokin Shari’a ko suka daure mutane bisa laifin batanci.
Sai dai mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci tattaunawar, ya ce wannan mataki na Amurka “ba daidai ba ne”, yana kuma iya haifar da rikici tsakanin kasashen biyu da kuma dagula dangantaka.
Wani ɗan majalisa daga Osun, Oluwole Oke, ya zargi majalisar Amurka da hana jami’an Najeriya halartar zaman sauraron kudirin, yana cewa hakan “na nufin bata sunan Najeriya”.
Majalisar ta kuma bukaci ‘yan majalisar Amurka da suka nuna damuwa da Najeriya da su shiga tattaunawa ta haɗin gwiwa domin fahimtar hakikanin gaskiya kan batun addini da tsaro a ƙasar.


