Kotu ta bayar da umurnin a kama tsohon shugaban hukumar INEC

0
20

Kotun Tarayya da ke Osogbo, jihar Osun, ta ba da umarnin a kama tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, bisa zargin raina umarnin kotu.

Hukuncin ya biyo bayan shigar da kara da jam’iyyar Action Alliance (AA) ta yi, inda ta zargi INEC da shugabanta da kin bin hukuncin kotu a shari’ar da ke da lamba FHC/OS/CS/194/2024, wadda Mai Shari’a Funmilola Demi-Ajayi ta yanke.

Rahotanni sun bayyana cewa Farfesa Yakubu ya riga ya mika takardar barin aiki bayan karewar wa’adinsa a matsayin shugaban INEC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here