Kaso 98 na yan Najeriya zasu daina biyan haraji daga shekarar 2026–Gwsmnati

0
23

Kaso 98 na yan Najeriya zasu daina biyan haraji daga shekarar 2026–Gwsmnati

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran haraji, Dr. Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa daga Janairu 2026, kashi 98% na ‘yan Najeriya za su daina biyan haraji ko kuma a rage musu harajin zuwa mafi ƙaranci.

Ya ce, wannan sabon tsarin zai taimaka wajen rage wa talakawa nauyin tattalin arziki, domin “ba za a iya cajar talakawa haraji ba a lokacin da suke fama da talauci.”

A cewar Oyedele, mutanen da ke samun ƙasa da ₦200,000 a wata ba za su biya haraji ba, yayin da kamfanonin da ke samun ƙasa da ₦100 miliyan a shekara suma za a cire su daga biyan haraji gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa an rage harajin manyan kamfanoni daga 30% zuwa 25%, domin ƙarfafa mutane su yi rajistar haraji da gwamnati.

Sabuwar dokar, wacce za ta fara aiki a 2026, na da nufin kare masu ƙaramin ƙarfi da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here