Gwamnatin Jihar Kano ta rufe otal-otal guda goma da ke cikin birnin Kano, ciki har da fitattun wurare irin su Sarina Suites da Horizon Hotel, bisa karya dokokin da ke tafiyar da harkokin yawon buɗe ido.
Babban Mai Dauko wa gwamnan Kano Rahoto a Ma’aikatar Yawon Buɗe Ido, Ibrahim Adam Bagwai, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, rufe otal-otal ɗin ya haɗa da Sarina Suites, Horizon Hotel, Blue Spot Hotel, da wasu otal guda bakwai da ke cikin jihar.
A cewar sanarwar, wannan mataki na cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa cibiyoyin yawon buɗe ido da masaukai suna bin ƙa’idojin gwamnati tare da kare mutuncin al’umma.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da sa ido kan dukkan otal-otal da wuraren shaƙatawa a jihar domin tabbatar da tsabta, tsaro, da kuma bin ƙa’idojin gwamnati.