EFCC na binciken Shugaban NAHCON kan zargin karkatar da Naira biliyan 50

0
27

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta kaddamar da bincike kan Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Saleh Abdullahi Usman, bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da ake zaton na da alaƙa da shirye-shiryen aikin Hajjin bana na 2025.

Rahotanni daga The Guardian Nigeria sun nuna cewa Farfesa Usman ya amsa gayyatar EFCC a ofishinta dake Abuja a ranar Talata, inda aka sake shi bayan bayar da beli, tare da umartar shi da ya rika bayyana a ofishin hukumar kullum yayin da bincike ke ci gaba.

Ana zargin cewa sama da Naira biliyan 50 ne aka karkatar daga kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da aikin Hajji, ciki har da Naira biliyan 25 da aka yi amfani da su wajen biyan kuɗin sansanonin Masha’ir ba tare da izini ba, da Naira biliyan 7.9 na wuraren zama na gaggawa, da kuma Naira biliyan 1.6 na kuɗin tafiya da ake cewa matan wasu jami’ai ne suka ci gajiyarsu.

A watan da ya gabata, EFCC ta kama Kwamishinan NAHCON mai kula da manufofi da harkokin ma’aikata da kuɗi, Aliu Abdulrazak, da kuma Daraktan Kudi da Lissafi, Aminu Y. Muhammad, bisa zargin hannu a wannan badakala.

Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa an dakatar da takardar shaidar tsaron Farfesa Usman a Villa har sai an kammala binciken abin da ke nuna muhimmancin da gwamnati ke bai wa lamarin.

A yayin wani zaman sauraron jama’a da Majalisar Wakilai ta shirya a baya-bayan nan, Shugaban NAHCON ya amince da cewa akwai wasu “mu’amaloli marasa tsafta” a cikin hukumar, amma ya yi alkawarin cewa za su bayar da haɗin kai wajen tabbatar da gaskiya da ɗa’a.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, NAHCON ta bayyana cewa ba za ta kare kowa ba idan aka same shi da laifi, tare da tabbatar da cewa za ta bayar da cikakken haɗin kai da EFCC da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa hukumar tana gudanar da bincike, amma ya ce za a fitar da cikakken bayani daga baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here