Dangote ya rage farashin gas ɗin girki

0
40

Matatar man fetur ta Dangote ta bayyana cewa ta rage farashin gas ɗin girki (LPG) zuwa Naira 715 a kowane kilo tun kusan watanni biyu da suka gabata, sabanin rahotannin da ke cewa an ƙara farashin zuwa Naira 760/kg.

Wata majiya daga cikin kamfanin ta tabbatar da cewa tun daga watan Agusta ake sayar da gas ɗin ga ‘yan kasuwa a farashin Naira 715,000 kowace metric ton, wanda yake daidai da Naira 715/kg.

Majiyar ta ce:

> “Idan aka ƙara kuɗin sufuri da wasu kuɗaɗe na dillalai, bai kamata farashin ya wuce Naira 800/kg ba.”

A cewar Bayo Ojulari, shugaban kamfanin NNPC Limited, hauhawar farashin gas ɗin a ‘yan kwanakin nan ya samo asali ne daga yajin aikin ma’aikatan PENGASSAN.

A wasu sassan Lagos, farashin gas ɗin ya kai har Naira 2,000/kg, amma an ce farashin zai sauka nan ba da jimawa ba bayan da tasirin yajin aikin ya lafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here