Babu mai tsoratar da mu, zaben 2027 na Allah ne–Abba

0
20

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ba ya jin tsoron barazana ko duk wani kalubale da ake yi masa game da zaben shekarar 2027, domin komai yana hannun Allah.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Gwamna Abba cikin fushi yana mayar da martani ga masu yin magana kan yiwuwar ya rasa nasara a 2027.

Ya ce, “Babu mai tsoratar da mu, 2027 ta Allah ce. Idan Allah ya ce, ko duniya gaba ɗaya ta taru, ba za ta iya hana hakan ba.”

Kalaman nasa na iya zama martani ga wasu malaman addini dake umartar magoya bayan su suyi rijistar zabe, saboda akwai wanda suke so a zaɓa a matsayin gwamnan Kano in lokacin zaɓen shekarar 2027, yazo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here