Ba daidai bane gwamnati ta amince a riƙa shigo da abinci daga ketare–Sarkin Kano

0
76

Mai Martaba Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya soki manufofin gwamnatin tarayya na shigo da abinci daga ƙasashen waje, yana mai cewa wannan mataki yana lalata harkar noma a cikin gida tare da barazana ga samar da abinci a cikin gida.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta News Central, a ranar Talata, Sanusi ya ce duk da cewa yana goyon bayan kusan kashi 80 cikin 100 na manufofin tattalin arzikin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, amma shigo da abinci don rage hauhawar farashi ba daidai ba ne.

> “An yi wannan shiri ne domin rage farashin abinci, amma sakamakon sa akasin haka ne. Yana hana manoma kwarin gwiwa kuma yana raunana harkar samar da kayayyaki a cikin gida,” in ji shi.

Sarkin ya yaba da wasu matakan gwamnatin Tinubu musamman a ɓangaren daidaita manufofin kudi da kasafin kuɗi, wanda a cewarsa ya taimaka wajen daidaita tattalin arzikin ƙasa. 

 “Ina goyon bayan kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na abin da gwamnati ke yi, sai dai batun shigo da abinci da kuma irin yadda ake kashe kuɗi ne kawai nake da damuwa a kai,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here