Hukumar gudanarwar ta gidan rediyon Guarantee FM 94.7 Kano ta nada Abubakar Balarabe Kofar Naisa a matsayin sabon Janar Manaja.
Kofar Naisa, wanda ya jima a fannin yada labarai da gudanar da kafafen watsa shirye-shirye, yana da gogewa wajen inganta ayyukan gidan rediyo.
Ana kyautata zaton naɗin nasa zai kara karfafa shugabanci da ci gaban kafar wajen isar da shirye-shiryen da ke ilmantarwa, nishadantarwa da fadakar da jama’a a Kano da kewayenta.
A yayin da ya karɓi ragamar tashar Kofar Naisa ya gode wa hukumar rediyon bisa amincewa da shi, tare da yin alkawarin yin aiki tukuru domin tabbatar da ci gaban gidan rediyon da kare darajar sana’ar yada labarai.