Ƴan sandan Akwa Ibom sun gargaɗi masu yin rawar gargajiya

0
48

Rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom ta sake gargadin al’umma game da ayyukan wasu masu rawar gargajiya ta (masquerade) da ke amfani da bukukuwan al’ada wajen aikata laifuka a sassan jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Baba Mohammed Azare, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ke mayar da bukukuwan al’ada hanyar yin tashin hankali, tsoratarwa, da karɓar kuɗi ta ƙarfi daga jama’a.

Rundunar ta ce duk da gargadin da ta bayar a ranar 18 ga Satumba, 2025, wasu daga cikin masu rawar gargajiyar sun ci gaba da fitowa ba tare da izini ba, suna cin zarafin jama’a, jikkata mutane, da kuma karɓar kuɗi a hannun su ta dole.

Saboda haka, rundunar ta jaddada cewa babu wanda ya dace ya shirya ko ya halarci biki ko fita rawar gargajiya ba tare da samun izini daga kwamishinan ƴan sanda ba kamar yadda doka ta tanada.

An kuma tunatar da shugabannin al’umma da masu shirya irin waɗannan bukukuwan cewa suna da nauyin tabbatar da bin doka da oda. Rundunar ta bayyana cewa waɗannan abubuwa suna daga cikin manyan laifuka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here