Tsarin bashin kuɗin karatu ya haifar da tsadar kuɗin rijistar ɗalibai–Rahoto

0
28

Hukumar bayar da tallafin kuɗin karatu ta Najeriya (NELFUND) ta bayyana damuwa kan yadda wasu jami’o’i ke ƙara kuɗin makaranta da ya kai tsakanin kashi 20 zuwa 521 cikin ɗari.

Wani rahoton hukumar ya nuna cewa karin kuɗin karatu, musamman a fannoni irin su likitanci, malaman jinya, da lauya, yana jefa ɗalibai cikin wahala tare da kawo cikas ga aikin hukumar.

A cewar rahoton mai taken “Tsarin rage illar ƙarin kuɗin makarantu,” jami’o’in da abin ya shafa sun haɗa da:

Jami’ar Ilesha ta Osun

Jami’ar Jihar Ekiti

Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Ondo

Jami’ar Edo

Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH), Oyo

Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta David Umahi (DUFUHS), Ebonyi

Wannan na zuwa ne watanni kaɗan bayan rahoton jaridar The Guardian da ya bayyana cewa jami’o’i 51 sun shiga cikin zargin cire kuɗi ba bisa ka’ida ba daga tsarin tallafin karatun.

A watan Yuli, rahoton ya kuma nuna cewa hukumar ta ki amincewa da buƙatun rance daga jami’o’i 10 saboda ƙarin kuɗin makaranta da ya kai har kashi 900 cikin ɗari.

Rahoton ya nuna misalan karin kuɗin kamar haka:

Jami’ar Ilesha: Kuɗin karatun ma’aikatan jinya ya tashi daga ₦825,000 zuwa ₦1.276m — ƙarin kashi 55%. Haka kuma fannin lauya ya tashi daga ₦1.276m zuwa ₦1.526m — ƙarin kashi 20%.

Jami’ar Jihar Ekiti: Fannin likitanci ya tashi daga ₦797,000 zuwa ₦1.132m — ƙarin kashi 42%.

Jami’ar Edo: Kuɗin likitanci ya tashi daga ₦3.25m zuwa ₦4.25m — ƙarin kashi 31%.

Wannan na nufin cewa ɗalibin likitanci a jami’ar Edo zai iya kammala karatu da bashin da ya kai sama da ₦51 miliyan.

Haka zalika, rahoton ya nuna cewa Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Ondo ta ƙara kuɗin karatu a wasu fannoni uku da ƙarin da ya kai tsakanin kashi 40 zuwa 149 cikin ɗari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here