Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da ajiye aikin da Farfesa Mahmood Yakubu ya yi a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), bayan kammala wa’adinsa na biyu.
A lokaci guda, shugaban ƙasar ya karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasa wato CON, saboda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
Farfesa Yakubu ya fara rike wannan mukami ne a watan Nuwamba na shekarar 2015, inda aka sake tabbatar da shi a karo na biyu a 2020. Wa’adinsa na biyu ya ƙare a bana.
Shugaba Tinubu ya gode masa bisa irin hidimar da ya bayar ga ƙasa, musamman wajen gudanar da zaɓuɓɓuka cikin lumana da gaskiya a lokacin shugabancinsa.