Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya mika wa May Agbamuche, ragamar shugabancin hukumar a matsayin mukaddashiyar shugaba.
Agbamuche ce tsohuwar kwamishina mafi tsawon lokaci a hukumar, kuma za ta riƙe mukamin har sai an naɗa sabon shugaba.
Yakubu ya sanar da hakan ne a wani taro da ya gudanar tare da kwamishinonin zabe na jihohi a shelkwatar hukumar da ke Abuja a yau Talata, inda ya nemi haɗin kai da goyon bayan ma’aikatan hukumar ga sabuwar mukaddashiyar shugaba.