Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta halarci zaman majalisar dattawan Najeriya a karon farko bayan dakatar da ita da aka yi na tsawon watanni shida.
Majalisar ta dawo bakin aiki ne a ranar Talata bayan É—an jinkirin komawa, inda mataimakin shugaban majalisar, Sanata Jibrin Barau, ya jagoranci zaman.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio wanda ake ganin shi ne abokin rikicin Natasha bai halarci zaman ba, koda yake ba a bayyana dalilin hakan ba.
Tun farko, dakatar da Natasha ya jawo cece-kuce a siyasar ƙasar nan, musamman bisa zargin cin zarafin da ake cewa ta yi wa shugaban majalisar.