Ministan Kimiyya ya yi murabus kan zargin jabun takardun karatu

0
30

Rahotanni daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus ɗin Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Geoffrey Uche Nnaji, bayan wasu zarge-zarge da ake yi masa kan jabun takardun karatu.

An nada Nnaji a watan Agusta, 2023, amma ya sanar da murabus dinsa a yau, inda ya mika wasiƙar godiya ga shugaban ƙasa bisa damar da ya ba shi ta yin hidima ga ƙasar nan.

A cikin wasiƙarsa, Nnaji ya bayyana cewa ya zama abin cin fuska da kazafi daga wasu abokan hamayya na siyasa, wanda hakan ne ya sa ya yanke shawarar barin mukaminsa.

Shugaba Tinubu ya yaba masa bisa irin gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake aiki, tare da yi masa fatan alheri a ayyukan da zai gudanar nan gaba.

Wannan sanarwa ta fito ne daga Bayo Onanuga, mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayani da dabarun sadarwa, kamar yadda ya wallafa a kafar X.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here