Majalisar Dattawa ta koma zaman ta a yau Talata, bayan hutun da ya wuce makonni biyu, domin ci gaba da tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro da gyaran dokar zabe.
Majalisar ta jinkirta dawowa daga ranar 23 ga Satumba zuwa 7 ga Oktoba, 2025, domin bai wa ‘yan majalisa damar halartar bukukuwan ranar ’yancin kan Najeriya da aka gudanar a ranar 1 ga Oktoba.
Daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna akwai shirin gudanar da taron koli kan tsaro, gyaran dokar zabe, kudirin sauya kundin tsarin mulki na 1999, da kuma kudirin kafa ofishin bincike da kasafin kudin majalisar wanda aka dade ana jiran amincewa da shi tsawon shekaru 20.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, zai jagoranci kwamitin da ke shirin taron tsaro, wanda zai duba hanyoyin magance karuwar matsalar rashin tsaro a sassan kasar.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa majalisar dattawa ta 10 ta tattauna sama da kudirori 800, ciki har da 26 daga fadar shugaban kasa, yayin da wasu 499 ke jiran karatu na biyu.
Sai dai masu suka suna zargin cewa yawan jinkiri da hutun majalisar na rage wa ‘yan kasa kwarin gwiwa, musamman ganin yadda matsalar tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ke kara ta’azzara.