Majalisa zata yi doka akan yan Crypto da masu POS

0
29

Majalisar Wakilai ta fara wani muhimmin yunƙuri domin sanya tsari da kulawa a harkokin hada-hadar kuɗaɗe ta intanet, musamman masu amfani da kirifto da na’urorin POS.

A ranar Litinin, Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya ƙaddamar da wani kwamiti na musamman da zai binciki yadda ake amfani da waɗannan hanyoyi wajen mu’amalar kuɗi, da kuma yadda gwamnati za ta tabbatar da tsaron su da bin doka.

Abbas ya bayyana cewa, matakin ya zama dole saboda yawaitar damfara da manyan laifukan intanet, ciki har da samar da kuɗaɗe don ta’addanci, ta hannun masu amfani da kirifto da POS.

Ya ƙara da cewa, rashin dokoki na musamman da ke tsara wannan fanni, da kuma sauye-sauyen fasaha da ke faruwa akai-akai, sun tilasta majalisar ɗaukar wannan mataki domin kariya ga jama’a da kuma tabbatar da adalci a mu’amalar kuɗi.

Ana sa ran kwamitin zai gudanar da zaman jin ra’ayoyi daga masana da hukumomin da abin ya shafa, domin tattara bayanai da za su taimaka wajen samar da dokar kula da hada-hadar kuɗaɗe ta intanet a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here