Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barrista Abdulkadir Kabiru Maude (SAN), ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kawo karshen jinkiri a shari’o’in laifuka, domin tabbatar da adalci cikin gaggawa.
Barrister Maude Minjibir ya bayyana haka ne yayin da yake zagayen kotunan jihar a ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, domin duba yadda lauyoyin gwamnati ke gudanar da aikinsu.
A cewarsa, ma’aikatar shari’a za ta ci gaba da tabbatar da cewa dukkan harkokin shari’a suna gudana bisa doka da oda, tare da buɗe kofa ga kowane ɗan ƙasa da ke da korafi domin neman hakkinsa.
Kwamishinan ya kai wannan ziyara ne tare da babban sakataren ma’aikatar da kuma wasu daraktoci domin ƙara sa ido kan aikin kotuna a jihar.