Hukumar Kwastam ta Najeriya ta saka lokacin zana jarrabawar daukar ma’aikata

0
22

Hukumar hana fasa ƙauri ta Najeriya (NCS) ta sanar da cewa za ta gudanar da jarrabawar daukar ma’aikata ta hanyar na’ura mai ƙwaƙwalwa wato Computer-Based Test (CBT) ga masu neman aikin Inspectorate da Customs Assistant Cadre a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025.

Sanarwar ta fito ne a shafukan X da Facebook na hukumar a ranar Talata, inda ta bayyana cewa wannan jarrabawa ita ce mataki na biyu a tsarin daukar ma’aikata, bayan gwajin da aka gudanar a ranar 4 ga Oktoba.

Hukumar ta ce an raba masu jarrabawa zuwa rukunai uku (A, B, da C), kuma dole ne kowanne ya duba rukuninsa, ranar da lokacin jarrabawa ta hanyar shiga https://updates.customs.gov.ng da lambar NIN dinsa.

 Hukumar tayi gargadi cewa duk wanda ya karya jadawalin da aka tsara na iya fuskantar kora daga tsarin.

NCS ta hana amfani da wayoyi, kalkuleta ko kowace irin na’ura yayin jarrabawar, tare da jan kunne kan yin login fiye da ɗaya ko canja window yayin gwajin.

Hukumar ta bayyana cewa wannan jarrabawa ta shafi matakan Inspectorate da Customs Assistant ne kawai, ba ta shafi Superintendent Cadre ba.

An bayyana cewa masu jarrabawa za su iya gudanar da gwajin daga kowanne wuri da suke, muddin suna da ingantaccen intanet, amma sai sun yi amfani da laptop ko desktop mai ɗauke da na’urar daukar hoto, domin tsarin bai dace da wayar hannu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here