Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan kasuwa kan amfani da sinadarai masu guba a kayan abinci

0
21

Hukumar kare hakkin masu amfani da kayyaki ta Ƙasa (FCCPC) ta gargadi masu harkar kayan abinci da su guji amfani da sinadarai masu guba wajen sarrafa abinci musamman kayan marmari, tana mai cewa hakan na jefa lafiyar ‘yan Najeriya cikin haɗari.

Wakiliyar Shugaban Hukumar, Dr. Nkechi Mba, ta bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai dangane da ingancin abinci.

Ta ce hukumar na lura da yadda ake amfani da sinadarai kamar calcium carbide, bromate, Sudan red, da formalin wajen nunar da ‘ya’yan itatuwa da adana abinci, abin da ke iya haddasa cututtuka masu tsanani.

Dr. Mba ta ce FCCPC na aiki tare da hukumomin NAFDAC, SON, da ma’aikatun gwamnati don tabbatar da cewa masu harkar abinci suna bin ƙa’idojin tsaron lafiyar al’umma da tsafta.

“Wanda ya fifita riba fiye da lafiyar jama’a, zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji ta.

Ta kuma shawarci masu sana’ar kayayyakin abinci da su bi ka’idoji, su tabbatar da tsafta, da kuma sanya bayanai masu dacewa a kan kayayyakin da suke siyar wa.

A cewarta, akwai bukatar jama’a su kasance masu lura da abincin da suke saya domin kare kansu da iyalansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here