An buƙaci kotu ta hana Jonathan tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027

0
37

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu buƙatar da aka gabatar mata, wacce ke neman hana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027 ko wani zaɓen shugaban ƙasa nan gaba.

Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ne ya shigar da ƙarar, inda ya roƙi kotun da ta dakatar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) daga karɓa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takara.

Mai ƙarar ya bayyana cewa Jonathan ya riga ya cika wa’adin da kundin tsarin mulki ya amince da shi, bayan da ya karasa mulkin marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua, sannan ya sake yin wa’adi guda bayan lashe zaɓen 2011.

A halin yanzu, ba a bayyana ranar da kotun za ta fara sauraron ƙarar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here