Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa samun takardar shaidar kammala sakandare (SSCE) ya wadatar wa kowane ɗan Najeriya da ke son tsayawa takara ko riƙe muƙamin siyasa.
Shehu Sani ya faɗi haka ne a ranar Litinin yayin da yake mayar da martani kan rahoton da ya bayyana cewa jami’ar Nsukka ta musanta taɓa bai wa Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, digiri, domin bai kammala karatu a cikin ta ba.
Sanatan ya shawarci ‘yan siyasa da su riƙa faɗin gaskiya game da takardun karatunsu, yana mai cewa ƙarya kan shaidar karatu na janyo wa mutane matsala.