Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da ta sake duba wa ta kuma rage kudaden aikin Hajji na 2026 saboda tsadar da jama’a ke kuka da ita.
A baya NAHCON ta kafa farashin aikin Hajji kamar haka:
Yankin Maiduguri–Yola (Yobe, Borno, Adamawa da Taraba): ₦8,318,336.67
Jihohin Arewa: ₦8,244,813.67
Jihohin Kudu: ₦8,561,013.67
Gwamnatin tarayya ta ce kudaden sun dogara ne da canjin dala na Naira 1,550, amma yanzu da Naira ke ƙaruwa, akwai damar rage farashin zuwa tsakanin ₦7.6m zuwa ₦7.7m.
Sabbin kudaden za su fito cikin kwanaki biyu masu zuwa idan jihohi suka gaggauta biyan kuɗin alhazansu.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Yaro, da Sakataren NAHCON, Dr. Mustapha Mohammad, sun yaba da matakin gwamnatin, suna mai cewa zai taimaka wa Musulmai da dama su samu damar yin aikin Hajji.