Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna rashin damuwa da matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Najeriya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce Shugaban ƙasa ya fi mai da hankali wajen halartar bukukuwa da tarukan siyasa, maimakon ɗaukar matakai na kare rayukan ‘yan ƙasa.
Jam’iyyar ta ce “Shugaba Tinubu ya fi damuwa da harkokin siyasa sama da kare rayukan talakawa,” tana mai misalta yadda ake ci gaba da kashe mutane da yin garkuwa da su a jihohi da dama — daga Kaduna zuwa Zamfara, Benuwe zuwa Neja, da Filato.
ADC ta kuma bayyana cewa sama da makarantu 180 ne aka rufe a Arewacin Najeriya saboda matsalar tsaro, abin da ya tilasta wa dubban yara zaman gida.
Haka kuma, jam’iyyar ta yi suka kan yadda Shugaban ƙasa ke aike wa da saƙonnin ta’aziyya bayan hare-hare, maimakon ɗaukar mataki kafin aukuwar su.
Ta ƙara da cewa duk da wannan yanayi, gwamnatin tarayya na ci gaba da cewa tana samun ci gaba — lamarin da ADC ta ce bai dace da gaskiyar halin da al’umma ke ciki ba.