Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya sake ɗaga farashin lita ɗaya na man fetur a wasu tashoshinsa dake Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa gidajen man NNPCL na Wuse Zone 6 da Zone 4 sun ƙara farashin daga Nairs 890 zuwa Nairs 905 a lita ƙarin Naita 15 wanda ya kai kusan kashi 1.7 cikin ɗari.
Shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN), Alhaji Abubakar Maigandi, ya danganta hauhawar farashin da tangardar da ta biyo bayan rikicin ƙungiyar ma’aikatan man fetur (PENGASSAN) da matatar Dangote.
A cewar Maigandi, wasu daga cikin mambobin ƙungiyar na ci gaba da sayar da fetur tsakanin Naira 885 da Naira 895 a lita.