Najeriya zata ƙara yawan ɗanyen man fetur da take haƙowa a kullum

0
23

Shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya bayyana cewa Najeriya na fatan ƙara yawan ɗanyen mai da take haƙowa a kowace rana, zuwa ganga miliyan 1.8 a kullum kafin ƙarshen shekarar 2025.

Ojulari ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ya ce gyare-gyaren da kamfanin ya gudanar a watannin Agusta da Satumba sun taimaka wajen inganta ayyukan samar da mai, tare da ƙara fatan cimma burin ƙasar nan a fannin mai kafin ƙarshen shekara.

> “Muna fatan cewa kafin ƙarshen shekarar nan, Najeriya za ta iya haƙo ganga miliyan ɗaya da dubu 800 na ɗanyen mai a kullum,” in ji Ojulari.

A halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa ƙasar na haƙo kusan ganga miliyan 1.71 a kullum, abin da ya sanya ta cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da ɗanyen mai a ƙungiyar OPEC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here